20 Yuli 2020 - 10:40
Shugaban Kasar Syria Da mai Dakinsa Sun Kada Kuri’ar Zaben ‘Yan Majalisar Dokokin Kasar

A yau Lahadi an bude dubban mazabu a fadin kasar Syria domin kada kuri’ar zaben “‘yan majalisar al’umma” ta kasar Syria, inda shugaban kasar Basshar Assad da mai dakinsa Asma’u, su ka kada nasu kuri’un.

ABNA24: An bude zaben ‘yan majalisa ne a kasar Syria wanda shi ne karo na uku, tun da kasar ta fada cikin yaki. Al’ummar kasar dai suna kada kuri’un nasu ne domin zabar wadanda za su wakilce su a majalisar al’umma wacce ita ce majalisar dokoki.

A cikin babban birnin kasar, Damascuss an samu masu kada kuri’a da dama, tare da la’akari da ka’idar bayar da tazara a tsakanin mutane domin kaucewa kamuwa da cutar corona.

A can birnin Halab ma, an sami cincirindon jama’a masu kada kuri’a,kamar yadda tashar talabijin din ‘almayadeen’ ta kasar Lebanon ta bayar da labari.

Da akwai ‘yan takara 1650 da suke gogayya da juna a cikin mazabu 15 a cikin birnin Damascuss.

Adadin kujerun da ake da su a majalisar kasar su ne 250.

342/